Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin shugaban ?asa Muhammadu Buhari na duba yiwuwar soke kungiyar malaman jami’a ta kasa wato ASUU idan ta ki janye yajin aikin da ta dade tana yi.
Gwamnatin ta kuma sanar da cewa ta amince a mika naira biliyan 100 ga bangaren ilimin jami’a karkashin wani yunkuri da ta ke yi na warware matsalolin da suka janyo yajin aikin. baya ga wannan, gwamnatin ta kuma ware naira biliyan 50 ga kungiyoyin malaman jami’an a matsayin alawus-alawus domin su raba tsakanin rassan kungiyoyin.
Idan ba a manta ba, ASUU ta tsunduma cikin wannan yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar kuma ta ci gaba da sabunta shi zuwa wannan watan da muke ciki.
Majiyoyi daban-daban sun shaida wa jaridar Vanguard cewa ma’aikatar Ilimi ta kasar za ta iya soke kungiyar ta ASUU gaba dayanta idan kungiyar malaman ta ki nuna dattaku kan kokarin da gwmnatin Najeriyar ke yi kan warware wannan batun.
