Zan Mayar Da Jami’o’in Tarayya Hannun Jihohi Idan Na Lashe Zabe – Atiku

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya lashi takobin mika wa gwamnatocin jihohi dukkan jami’o’in da ke karkashin kulawar gwamantin tarayyar kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Atiku na jawabi ne yayin wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a babban birnin jihar Legas Ikeja.

Jaridar daily Trust ta ruwaito Atikun na cewa kadarorin da Najeriya ta mallaka na iya karewa nan ba da dadewa ba:

“Daya daga cikin abubuwan da na shirya yi shi ne karfafa wa bangaren ‘yan kasuwa – na cikin gida da na waje – da su zuba jari a banagren ilimi domin Najeriya ba ta da kadarorin da za su dade tana sarrafa su kamar yadda take yi a yanzu.”

Ya kuma yi tsokaci kan talaucin da ya addabi yawancin ‘yan kasar, yana cewa “tun bayan da Najeriya ta koma bisa turbar dimokradiyya a 1998/99, kasar ba ta taba samun kanta cikin tasko kamar wanda ta ke ciki ba a yanzu.”

Related posts

Leave a Comment