Yadda Aka Rika Wasoson Dukiyar Kasa Da Sunan Biyan Kwangila A Makon Karshe Na Mulkin Buhari

Muhammadu Buhari, President of the Federal Republic of Nigeria (cropped3)

Kwanaki biyar kafin cikar wa’adin mulkin tsohon Shugaban ?asa Muhammadu Buhari, Hukumar Raya Ilmin Manyan Makarantu (TETFund), ta bayar da kwangilar Naira biliyan 3.8, (N3,812,500,000) ba tare da bin ?a’ida ba.

An kamfaci ku?a?en an biya ba tare da an yi kwangilar ba tare da alamar aiwatar da ko ka?an na kwangilar ba.

PREMIUM TIMES ta banka?o yadda TETFund ta biya Naira biliyan 2.9 (2,932,032,516.28) a ranar 30 ga Yuni da 17 ga Nuwamba, 2023.

TETFund ta kamfaci ku?a?en daga cikin asusun ayyukan kasafin 2023, wa?anda aka ware domin yin wasu ayyuka a manyan makarantu 251 a cikin fa?in ?asar nan.

Ku?a?en na ayyukan rarar kasafin 2023 ?in dai Naira biliyan 15.2 ne. Amma maimakon TETFund ta sakar wa makarantun ku?a?en, kamar yadda doka ta tanadar, sai hukumar ta cire kaso 50 bisa 100 na ku?a?en, daga kowace makaranta. Ku?i sun tashi Naira biliyan 7.6 kenan.

An gano cewa TETFund ba ta buga tandar neman ‘yan kwangilar da za su yi gasar neman kwangilar ba, kamar yadda dokar bayar da kwangiloli ta ?asa ta tanadar.

Sannan kuma babu amincewar Majalisar Zartaswa ko shi kan sa Shugaban ?asa.

TETFund ta bayar da kwangilar bogin ce ga wani kamfani mai suna Fides Et Ratio Academy.

Wannan kamfani dai na gidoga ne, domin ko shafin yanar gizo ba shi da shi a intanet. Amma dai TETFund ta ce “kamfanin Lasisin IP ne mallakar Farfesa Klaus Stierstorfer ne.”

Takardar bayar da kwangilar ta na ?auke da sa hannun amincewar Daraktan Ayyukan Musamman, Kolopo Akulana.

An tuntu?i Hukumar Tantance Ha?i?anin Adadin Ku?a?en Kwangila (BPE), amma ta ce ba ta san da labarin bayar da kwangilar ba, kuma ba a tuntu?i Ofishin BPE domin ya tantance ku?a?en kwangilar kamar yadda doka ta tanadar ba.

An dan?ara wa kamfanin da aka ce an bai wa kwangilar Naira 550 a ranar 30 ga Yuni, 2023, a asusun bankin sa na Fedility Bank.

Kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya amince a tura ku?a?en kamar yadda lambar tura ku?a?en ta nuna, wato CBN/PROJ/224/JUN2023.

Ranar 12 ga Yuli kuma aka tura Naira miliyan 820, kuma ranar 26 ga Yuli aka tura Naira biliyan 1.5, sai kuma ranar 17 ga Nuwamba aka tura Naira miliyan 62, kuma duk CBN ke tura ku?a?en bisa umarni da amincewar TETFund.

Related posts

Leave a Comment