A ranar Alhamis 15/9/2022, Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero, ya amince da nadin babban Malamin addinin musulunci Sheik Ibrahim Daurawa, a matsayin sabon limamin masallacin juma’a na makarantar Skyline University, dake cikin birnin Kano.
Malam Daurawa wanda ya yi fice wajen hidimta wa musulunci da karantar da al’umma addini. Mutane daga kowanne bangare suna masu nuna farin cikinsu tare da fatan alkhairi domin an ajiye Kwarya a gurbinta.
Ni Indabawa Aliyu Imam ba ni da Malamin da nake kauna da amfanuwa da shi sama da Malam Daurawa. Sheikh Daurawa hafizin Alqur’ani ne masanin Sira da shari’ar musulunci yana daga malamai kalilan da suka rage a Najeriya wadanda suka yi nutso a kogin ilmin Fiqhu.
Hakika Malam Daurawa sha kundum ne a kowanne bangare na ilmi. Na jima ban ga Malamin da Allah ya ba shi fahimtar bangarorin ilmin addini da yawa ba kamar Malam Daurawa, idan yana karatu a kowanne bangare na ilmi sai mutum ya yi zaton bangaren kadai ya karanta.
Usulubin da’awar Malam ya sha bamban da usulubin Malamai da dama. Malam Daurawa karatu yake cike da ikhlasi don isar da sakon Manzon Allah S.A.W wanda kuma ya shagaltu da da’awa zuwa ga addinin musulunci da kokarin sulhu tsakanin ma’aurata da sauran jama’a, wannan ya sa da yawan ‘yan Dariqa ke kaunar Malam suna sauraron karatukansa masu cike da fa’ida da ilmantarwa. Yana da kyau ace gwamnoni masu kishin musulunci da su zakulo malaman da suka yi kamanceceniya da Malam Daurawa wajen ganin musulunci ya sami ci gaba.
