Ya Kamata A Zurfafa Bincike Kan Fa?uwar Jirgin Shugaban Dakarun Soji – ?ungiyar Arewa

An yi kira ga gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gudanar da cikakken bincike domin gano makasudin faruwar hatsarin jirgin saman dakarun soji wanda ya yi sanadin mutuwar Shugaban Dakarun Soji da wasu Sojoji a Kaduna.

Kiran ya fito ne daga bakin ?aya daga cikin Shugabannin ?ungiyar cigaban yankin Arewacin Najeriya Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Kaduna.

Gujungu ya ?ara da cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da yadda ake ta samun jita jita da kananan maganganu akan faruwar hatsarin wa?anda ke sanya damuwa, to wannan ba abu bane da za’a yi shiru akai ya zama wajibi ga gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin dake faruwa.

“A fili yake marigayi Janar Attahiru ya ?auko hanyar gyara ta fuskar inganta tsaro a ?asar nan, sannan a lokaci guda mutuwa ta ?auke shi tare da wasu mataimakan shi akan wannan fanni, dole jama’a su zargi wani abu kuma ya dace a gaggauta gudanar da bincike akai”.

Gujungu ya kuma koka da nuna damuwa dangane da yadda sashin Kudancin Najeriya ke murna da mutuwar shugaban Dakarun Sojin, inda yace wannan abin takaici ne kuma ya nuna a fili cewa kasarmu na fuskantar barazana ta kasancewa dunkulalliya, domin a tsarin aikin soja bai kamata ?angaranci ya shigo ciki ba, aiki ne na kishi da cigaban ?asa, yayin da aka wayi gari wasu na murna da mutuwar wani jagora a rundunar soji domin kawai bai fito daga yankin su ba babu shakka ana cikin hatsari.

Related posts

Leave a Comment