Wasanni: Wikki Ta Tsallake Siradi Da Kyar

Kungiyar kwallon kafa mallakar Jihar Bauchi, (Wikki Tourists), ta Tsallake Siradin da ya bata tabbacin ci gaba da buga gasar wassanin kwararro na kwalon kafa a Najeriya, biyo bayan lallasa takwararta (Adamawa United) daci biyu da nema 2-0 a folin wasa na tunawa da Sir. Abubakar Tafawa Balewa a garin Bauchi.

Dan wasan Wikki na gaba, mai suna Musa da Nazifi Yahaya sune suka samu nasarar zurara kwallayen biyu a cikin ragar Adamawa United cikin mintuna ashirin da biyu da Kuma minti arba’in 40 duk kafin aje hoton rabin lokaci.

Kafin dai wan nan wasa Kungiyar kwallon kafa ta Wikki cikin ta ya duri ruwa, suna ganin har in basu samu cikakken maki uku a wasan ba to sai dai su jira wani shekarar kakar wassanin, inda magoya bayan wikkin suke ta lissafin in har United ta rike su akayi chajaras, zata faru ta kare kenan, sai Kuma daga baya Suka samu nasara lashe wasan, ci biyu da nema.

Kuma har ila yau Kungiyar kwallon na Wikki tare da magoya bayansu ba haka suka ba, a fatan Kungiyar ta kasance ba, a cikin zullumi da kuma addu’ar samun nasara don su kara maki a kan teburin gasar kwallon kafar.

kocin Kungiyar wikkin kuwa Abdullahi Adamu jim kadan bayan kammala wasan, ya bayyana ma Muryar Yanci’ cewa samun nasarar ya biyo bayan yadda Kungiyar ta samu kanta a cikin tsaka mai wuya ne, domin shine wasa karo na talatin da takwas 38 kuma na karshe Wanda in ta samu galaba to ta tsallake in kuma akasamu akasi to saidai su rika kallo a akwatin nan talabijin a shekara na gaba, a gasar.

Bugu da kari kakakin Kungiyar Malam Nasiru Kobi, ya shaida ma manema labarai, a halin da ake ciki Kungiyar kwallon Wikki ta karkare gasaar da maki 45 daga wasanin gida da waje 38

A daya hannun kuwa hukumar gudanarwa ta Kungiyar Wikkin, sun yaba ma Gwamnati Jihar da basu goyon baya dari bisa dari ta wajen biyan su hakkokinsu na yan wasa, da Kuma alkawarin zage damtse a Sabon kakar wassanin da ke nan tafe.

Tuni dai a yanzu kungiyoyin kowa ya san matsayinsa a cikin gasar kwararron da aka kammala, na shekarar 2020/2021.

Daga karshe sunyi was magoya bayansu godiya da Kuma jajircewan da kasan cewa tare da kungiyar komai wahala.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment