Zan Canza Taku Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda – Sabon Shugaban Sojin Sama

Sabon hafsan rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Hassan Bala Abubakar, ya shiga Ofis ya fara aiki a sabon mu?amin da shugaban kasa ya na?a shi.

An ruwaito cewa Oladayo Amao, tsohon shugaban rundunar sojin saman ne ya mi?a wa Abubakar tuta a wani ?an kwarkwaryar biki da aka shirya a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Idan baku manta ba, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa hafsoshin tsaron Najeriya har da sifetan yan sanda na ?asa ritaya ranar Litinin da ya gabata.

A wata sanarwa da sakataren gwamnati, George Akume, ya sanya wa hannu, Tinubu ya kuma na?a sabbin shugabannin tsaro, inda aka ga sunan Abubakar a matsayin shugaban sojin sama.

AVM Abubakar ya yi alkawarin ?ara ?arfafa rundunar sojin sama a ?o?arin ya?i da ta’addaci, ayyukan yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi ?asar nan.

Ya kuma sha alwashin cewa zai ci gaba da ?ara yauka?a kyakkyawar dangantaka da ha?in guiwar rundunar sojin sama da sauran hukumomin tsaro kamar yadda ya taras, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A kalamansa, Abubakar ya ce:

“Tare da ha?in kan abokan aikina zamu ?ora daga abinda muka taras kan umarnin da shugaban ?asa ya bamu a lokacin zaman majalisar tsaron Najeriya.”

“Za kuma mu ?ara kawo sabbin hanyoyi da ?aukar matakai wa?anda zasu taka rawa wajen kawo karshen kalubalen da muke fama da su kuma su inganta ayyukan dakarunmu.”

Related posts

Leave a Comment