An bayyana cewar ko shakka babu da akwai ayoyin tambaya dangane da matakan da Kotu ta dauka akan jajirtaccen Dan sanda Abba Kyari da kuma umarnin da Shugaban ‘yan sanda ya bayar na sauke shi da maye gurbin shi da wani.
Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya ne suka bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da suka kira a garin Kaduna a karshen mako.
Gamayyar kungiyoyin sun ?ara da cewar ga duk wani ?an Najeriya mai kishin kasa ya sani kuma ya yarda cewar DCP Abba Kyari ?an sanda ne abin alfahari wanda ya tsayu wajen ganin al’amurra sun daidaita a ?asa, ta hanyar sanya kafar wando guda da duk wani tsagera a fadin Najeriya.
“Kyari ya bayar da gagarumar gudummawa wadda kowa ya yaba da ita wajen fasa garken bata gari musamman na sashin kudancin kasar nan, wanda hakan ya sa suka kullace shi har abin da ya faru yanzu ya faru.
Gamayyar kungiyoyin na Arewa ta bakin mai magana da yawun su Suleman Abdul-Aziz sun bayyana cewar dole masu hankali su yi zargin da akwai manakisa akan matakan da aka ?auka akan Kyari, duba da yadda Kotu ta bada Umarnin cewa a kamoshi, sannan aka yi gaggawar sauke shi daga mukaminsa.
Gamayyar kungiyoyin sun yi kira da babbar murya akan abi tsari da dokoki a yayin gudanar da bincike akan Abba Kyari ba a sanya son zuciya ba.
