Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ”shine fitatcen dan kwallo a duniya” a yanzu in ji tsohon dan wasan Blackburn Rovers, Chris Sutton.
Alan Shearer ya kwatanta kwallon da Salah ya ci Manchester City da ”daya ce da aka zura a raga mafi kayatarwa a Premier League a karni.
Dan wasan tawagar Masar, mai shekara 29 ya ci kwallo tara a wasa tara a kakar bana a Liverpool.
”A dai wannan lokacin yana kan gaba a kan Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo,” in ji Sutton.
Shi kuwa kocin Liverpool, Jurgen Kloop cewa ya yi za a dunga tuna kwallon da Salah ya zura a ragar City nan da shekara 60.
Bayan da ya ci kwallo na 100 a gasar Premier Cikin watan Satumba, Salah ne ya bai wa Sadio Mane kwallon da ya fara cin City a Anfield ranar Asabar.
Daga baya ne Salah ya zura ta sa a raga, koda yake Phil Foden da kuma Kevin de Bruyne ne suka farke wa City kwallayen da aka tashi wasan 2-2.
Sutton ya ce yadda Salah ke kan ganiya da cin kwallaye yau da gobe ne ya sa yake kan gaba a taka leda a duniya.
Bayan kwallo tara a karawa tara da ya yi wa Liverpool a dukkan fafatawa a bana, wanda kawo yanzu bai tsawaita kwantiraginsa a Anfield ba – ya bayar da guda uku aka zura a raga a kakar nan.
Tsohon dan wasan Chelsea kan ci kwallo 21 a kowacce kakar tamaula a Premier uku baya, wanda ya zazzaga 32 a raga a kakar 2017/18
Cikin kididdigar da aka fitar Salah ya yi wasa 165 da cin kwallo 103 aka yi nasara da shi a karawa 111 da rashin nasara a wasa 21 da bayar da kwallo 37 aka zura a raga da kai hari da ya nufi raga karo 265 da yayi.
