Shekarar Musulunci: An Shawarci Musulmi Su Sanya Kasa Cikin Addu’a

A yayin da aka shiga sabuwar shekarar addinin Musulunci wato yau 1 -1-1444 bayan hijiran Manzon Allah ( S .A. W) daga Makka zuwa Madina, an kirayi Al’umma Musulmi da su kara kaimi wajen yin addu’o’i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin matsalolin tsaro dake addabar kasan nan baki daya.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na arewacin Najeriya kuma Galadiman cika soron Adamawa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a zantawarsa da wakilinmu a Yola.

Alhaji Muhammed Ibrahim yace ya kamata al’umma Musulmi su sani sabuwar shekara ta addinin Musulunci tana da muhimmanci ga al’ummar musulmi saboda haka ya kamata al’umma Musulmi su zage damtse wajen gudanar da adduo’i dama aikata kyawawan ayyuka domin neman tsira ranar gobe kiyama.

Ya kuma shawarci al’umma Musulmi da su kaucewa dukkanin abin da zai kawo batanci ga addinin musulunci domin a cewarsa addinin musulunci addini ne dake wanzar da zaman lafiya da hadin kai tausayawa da dai sauransu.

Harwayau ya kirayi malamai da suyi amfani da wanna lokaci wajen fadakar da al’umma Musulmi muhimmanci wannan rana na shiga sabuwar shekarar addinin musulunci tare da shirya addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a fadin kasa baki daya.

86 ya kuma yi addu’ar Allah ya hada kan Al’umma musulmin duniya, ya kuma sa an shiga sabuwar shekaran addinin musulunci lafiya, da kuma samun dukkanin alheran da ke cikinta tare da yin fatan Allah madaukakin sarki ya sa a kammala Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku cikin kwanciya hankali ba tare da matsalaba.

Sannan ya roki Allah madaukakin sarki da ya zabawa Najeriya shugabanni masu adalci da tausayawa Al’umma, wadanda zasu kawo cigaba dama zaman lafiya a cikin kasan nan baki daya.

Related posts

Leave a Comment