Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta mayar da martani kan rahotannin da ke cewa hukumar EFCC ta cafke matar Gwamna Farfesa Hafsat Ganduje, tana mai cewa labarai ne kawai wadanda ‘yan adawa ke daukar nauyin sa.
A cewar wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya nuna nadama kan jita-jitar, inda ya kara da cewa ba za a iya bin diddigin labarin da ba shi da tushe daga wani tushe mai kyau ba kamar dai hukumar EFCC kanta.
Ya bayyana cewa abin takaici, an yada labaran karya a kafafen sada zumunta ba tare da tabbatarwa daga gwamnati ko hukumar hana almundahanar ba, wannan tsagwaron rashin adalci ne da kuma son kai inji shi.
“Ba a kama matar gwamnan ko aka tsare ta ba kuma a halin yanzu tana nan tana sauke nauyin da ke kanta.” Kwamishinan ya yi kira ga mutanen kirki na jihar da su yi watsi da jita-jitar, inda ya bukace su da su kwantar da hankalinsu.
Tunda farko dai EFCC ta gayyaci matar Gandujen zuwa hedkwatar ta a ranar 13 ga watan Satumba kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Amma bata amsa gayyatar ba kuma EFCC ta yi barazanar kama ta. Majiyoyi na kusa da ita daga baya sun bayyana cewa ta tafi Birtaniya ne domin hallartar bikin kammala karatun danta.
