Kungiyar tabbatar da adalci ta Arewacin Najeriya NNTG a takaice ta yi kira da babbar murya ga shugaban ?asa Buhari da ministan shari’a Abubakar Malami da yin gaggawar umartar kwamitin dake bincikar tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu su sake shi nan take.
A cikin wata takardar sanarwa da shugaban kungiyar na ?asa Kwamared Musa Muhammad ya sanya wa hannu, sun ?alubalanci ministan Shari’a Abubakar Malami da kokarin keta haddin Magu bisa ga wasu dalilai na son zuciya, wanda ya bayyana ga ‘yan Najeriya shi mutumin kirki ne.
Kungiyar sun yi kira ga kwamitin dake bincikar Magu, da su gudanar da bincike na gaskiya akan Magu wanda kowa ya sani shi mutumin kirki ne mai ya?i da cin hanci da rashawa, wanda da akwai ?arayin gwamnati da dama da aka samu da sata dumu-dumu amma an sake su.
“Shin Magu ne ka?ai wanda ake tuhuma da zargin cin hanci da rashawa, amma me ya sa kwamitin ya ?auki zafi akan Magu shi kadai? Wannan ya tabbatar da cewar da akwai wata manakisa da ake shiryawa.
A watan Satumban 2020 mai Shari’a Ayo Salami dake jagorantar bincikar Magu ya bayyana cewar ya yi nadamar jagorantar kwamitin binciken sakamakon zarge zargen ba su da tushe ballantana makama.
Salami ya bayyana hakan a wani zaman sirri da aka yi kan batun Magu a fadar shugaban kasa wanda aka hana ‘yan Jarida shiga ciki, amma daga bisani wasu lauyoyi da suka halarci zaman sun fallasa abin da ya faru.
Kungiyoyin kare hakkin ?an Adam da masu fashin ba?in al’amurra sun yi ta kiran da a rin?a gudanar da zaman kwamitin binciken a bainar Jama’a domin samun daidaito da adalci amma aka yi watsi da wannan kiran.
“Lallai mahukunta su guji sanya son zuciya a yayin gudanar da bincike musamman akan abin da ya shafi cin rashawa”.
