Daya daga cikin mawakan siyasa Ummi Kano, ta bayyana cewa, a da ita ba kowa ba ce, babu wanda ya san da ita, amma a yanzu ta sanadiyyar waka ta yi suna a duniya.
Mawakiya Ummi Kano ta yi bayanin hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimokuradiyya, a lokacin da ya ke yi mata tambaya, game da irin nasarar da ta samu a matsayin ta na Mawakiya.
Sai ta fara da cewa “Ai ni waka ta yi mini rana, domin babu abin da ban samu ba a harkar waka, don sanadiyyar waka na yi Mota na yi gida, kuma na fita kasashen waje, duk ta dalilin waka.” Inji ta.
Ummi Kano ta cigaba da cewar “Ni tun da farko na fara waka ne, tun ina karama a makarantar Islamiyya, to daga baya sai aka yi mini aure, kuma bayan aure na ya mutu, sai na dawo na ci gaba da yin wakar, tun ina yin ta yabon Manzon Allah S.A.W, wadda maigida Tijjani Gandu ya ke koya mun, sai kuma na zo na ke wakokin soyayya, kuma daga nan sai na shiga wakokin siyasa tare da Tijjani Gandu, don duk wakokin sa ni ce na ke yi masa amshi, shi ya sa aka fi sani na da wakar Abba Gida Gida.” A cewar ta.
Ta ci gaba da cewar” Waka sana’a ta ce, kuma ina alfahari da ita, domin waka ta yi mini komai a rayuwa, babu abin da ba ta yi mini ba, a yanzu sai dai fatan cikawa da imani.” Inji Ummi.
Baya ga Nasarori da Ummi Kano ta samu a harkar waka, ko akwai wata matsalar da ta ci karo da ita a harkar?
Sai ta ce “Babba ma kuwa, domin ta sanadiyyar waka, har sai da aka yi yunkurin a kashe ni, don akwai wani lokaci da ina tafiya sai kawai na hadu da wasu yan daba, su ka rinka yanka ta da wukake, wanda in banda Allah ya tsallakar da ni, da sai dai a dauki gawa ta a wajen, don ba su yi niyyar su bar ni da rai ba, to wannan duk ta sanadiyyar waka ne, don haka na samu nasara, kuma na ci karo da matsala a harkar waka, kuma wannan darasi ne na rayuwa. ” Kamar yadda ta bayyana.
Daga karshe Ummi Kano ta yi kira da abokan sana’ar ta na waka da cewar, su sani duk inda nasara take, to akwai kalubale, don haka su cigaba da sana’ar su kada su karaya.
