Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Nasiru El Rufa’i ta garga?i ?ungiyar Kwadago NLC game da yajin aikin da take jagoranta inda ta ce yajin aikin ya ci karo da dokar ?wadago.
“Dokar ta kuma haramta ?untatawa duk wani mutum daga gudanar da harkokinsa saboda yajin aikin.”
Bisa ga haka gwamnatin jihar Kaduna za ta kare dukkanin cibiyoyinta da kuma ikon ma’aikata na shiga wuraren ayyukansu.
Ta kara da cewa dokokin kungiyar kwadago a Najeriya ba su lamunci rashin tsari ba,”
Mutane kuma sun shiga shafukan sada zumunta domin bayyana ra’ayinsu kan yajin aikin NLC a jihar.
Gwamnan jihar Kaduna ya mayar da martani ga wani sakon Tuwita da ke ikirarin cewa yajin aikin zai zama irin wanda ba a taba yi ba a jihar.
Sakon na cewa gwamnan na shirin kama shugaban kungiyar kwadago.
Gwamnan jihar Kaduna ya mayar da martani inda ya ce su ne iyayen munafukai kuma gwamnatinsa na nan tana jiransu.
