Gamayyar ?ungiyoyin ma’aikata shiyyar Arewa maso yamma masu ya?i da cin hanci da rashawa wato “NorthWest Coalition For Anti-Corruption Civil Society Organization” a turance sun jadadda goyon baya ga shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa tare da yin watsi da dukkanin wani yunkuri na cire shi daga kan mu?amin sa.
Da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai da gamayyar ?ungiyoyin suka kira a Kaduna mai magana da yawun Kungiyoyin Hamza Abidina ?an Liman ya bayyana cewar hankalin su ya kai bisa ga wani yunkuri da wasu baragurbi wa?anda ke da hannu dumu-dumu a badakalar cin hanci da rashawa a ?asar nan ke yi na ganin bayan shugaban hukumar ta EFCC wanda ya dage wajen ya?i da cin hanci da rashawa a fa?in ?asar.
“A tsawon shekaru biyu da Abdulrasheed Bawa ya yi a matsayin shugaban EFCC ya aikata ayyuka na cigaba a hukumar wajen zakulo da banka?o ?arayin Gwamnati, wanda ya kamata ‘yan Najeriya su ha?a hannu gaba ?aya wajen taimakawa ?o?arin sa na ciyar da kasa gaba’.
Abidina ?an Liman ya ce nan gaba kadan ba da Jimawa ba za su fallasa sunayen masu yunkurin kawo matsala da kutungwilar cire Bawa daga mu?amin sa, inda suka yi kira ga shugaban ?asa Muhammadu Buhari da yin watsi da dukkanin wani yunkurin cire Abdulrasheed Bawa daga mu?amin sa.
