Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban alkalan Najeriya (CJN), Justice Tanko Muhammad ya tattaro manyan alkalan jihar River, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa akan rikicin shari’ar jam’iyyar adawa ta PDP.
An ruwaito cewa, wannan ya biyo bayan hukuci mabanbanta da ko wannensu ya yanke a jiharsa masu karo da juna. A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna dangane da rikicin da ya barko jam’iyyar PDP.
Yayin da babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da Uche Secondus daga zama shugaban jam’iyyar na kasa, sai kuma kotun jihar Kebbi ta dawo da shi. Sannan akwai hukunce-hukuncen da suka danganci wasu jam’iyoyin wadanda suke kawo rikici.
A takardar gayyatar ta ranar 30 ga watan Augustan 2021 da shugaban alkalan ya aika don gayyatar alkalan, ya na bukatar su bayyana a gaban sa don zaunawa a kan wadannan hukunce-hukuncen.
“An janyo hankalina a kan illolin da hukunce-hukuncen da wasu kotu suka yanke wanda ko wanne ya ci karo da wani. Don haka ya zama tilas a kaina in gayyace ku don mu zauna mu tattauna a kan wannan lamarin”.
