Uwargidan Shugaban Kasa Ta Kalubalanci Pantami

Rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari a ranar Lahadi 12 ga watan Satumba ta yada wani bidiyon da ke nuna Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami, yana kuka yayin daya daga cikin wa’azinsa na baya-bayan nan.

Pantami ya kasance mai yawan kuka yayin zaman tafsirinsa lokacin da ake karanta wasu ayoyi a cikin Al?ur’ani Mai Girma, ko lokacin da yake bayanin musgunawa Musulmi.

Aisha Buhari ta yada bidiyon a shafinta na Instagram tare da wata sanarwa mai tsauri: “A cire tsoro a yi abinda ya dace”.

A cikin gajeren bidiyon, Pantami da mai ja masa baki sun fashe da kuka lokacin da ministan ya nemi mai karatun ya karanta wata aya akan tsoron Allah.

Alaramma mai jan baki ya jawo aya ta 63 ta Suratu Maryam, ayar da ke magana kan sakamakon da Allah zai yi wa bayinsa masu tsoron Allah. Yayin da Pantami ya fara sharhin ayar, shi ma ya fashe da kuka, yana cewa: “Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu. Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu. Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu.”

Uwargidan shugaban kasa ta shahara wajen sukar gwamnatin mijinta da wasu masu nade-naden gwamnatinsa. Ba sau daya ba, an sha samun maganganu da dama na Aisha Buhari inda take sukar gwamnatin Buhari da wasu mukarrabansa.

A wata hira da BBC a 2016, Aisha Buhari ta bayyana yadda wasu kalilan din mutane suka zagaye Shugaba Buhari, kuma su kadai suke amfana. A cewarta, shugaban bai san yawancin jami’an da ya ke nadawa ba.

Related posts

Leave a Comment