?etare: Matan Afghanistan Sun Goyi Bayan Taliban

Yayin da duniya ke ganin Taliban za su wulakanta mata, sai ga mata a kasar sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Taliban Wannan ya faru ne a ranar Asabar a bikin cika shekara 20 na kai hari kan cibiyar kasuwanci dake Amurka a 11/9.

Mata da dama sun fito rike da tutoci suna nuna goyon baya ga Talihan tare da yin kabbara ga kungiyar.

Daruruwan mata, sanye da bakaken kaya, sun yi maci a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, dauke da alamun nuna goyon baya ga kungiyar Taliban, kamar yadda rahoton Al Arabiya ya fada a ranar Asabar 11 ga watan Satumba.

Mata da dama, wadanda suka lullube daga kai har zuwa kafa kuma suka lullube fuskokinsu, sun yi zanga-zanga a waje da cikin Jami’ar Ilimi ta Shaheed Rabbani, dauke da tutocin Taliban.

Related posts

Leave a Comment