Tsohuwar Ministar Mata Mama Taraba Ta Rasu

Mun samu labarin rasuwar tsohuwar ministar ma’aikatar Mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan bayan fama da doguwar rashin lafiya da ta yi.

Wata majiya ta shaida mana cewa tsohuwar ministar ta rasu ne a wani asbiti da ke birnin al-Kahira na Masar bayan fama da wata gajeriayar rashin lafiya.

Marigayiyar wadda aka fi sani da ‘Mama Taraba’ ta rike mukamin Sanata mai wakiltar Taraba ta Arewa.

Ta yi takarar gwamnan Jihar Taraba a zaben 2015.

Kuma ta kara yin takarar wannan matsayi a jam’iyyar UDP a zaben 2019.

An haifi marigayiya Aisha Al-Hassan a ranar 16 ga watan Satumbar 1959 a Jalingo dake jihar Taraba.

Related posts

Leave a Comment