An bayyana cewar sakamakon wata ?ididdiga da bincike da aka gudanar an gano kimanin mutane Dubu 300 ne bala’in rikicin manoma da makiyaya ya raba da muhallinsu a yankin Arewacin Najeriya, kuma ?aruwar adadin al?aluman na da tada tayar da hankali matuka.
Wata ?ungiyar bincike mai zaman kanta a tarayyar Najeriya Zinariya Consult ta fitar da sakamakon inda ta ?iyasta cewa sama da mutum dubu 300 sun rasa muhallansu a jihohi 4 na ?asar sakamakon rikicin manoma da makiyaya a fa?in Najeriya.
Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa ?aya daga cikin jagororin binciken, Dr Joseph Ochogwu, ne ya shaida hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai.
A cewar Ochogwu in ji jaridar, jihohin da ke fuskantar ?aruwar irin wannan rikici sun hada da Benue da Plateau da Nasarawa da Taraba da Adamawa da Kaduna.
Wannan yanayi da ake ciki ya haifar da rasa rayuka da asarar dukiyoyi da raba dubbai da muhallansu.
Rikicin manoma da makiyaya rikici ne wanda ya da?e yana ci wa jama’a tuwo a ?warya musanman a yankin Arewacin Najeriya, inda ke haifar da asarar tarin dukiyoyi da rayuka a kusan kowace shekara.
Daga bisani rikicin ya sauya salo inda ya koma ta’addancin ‘yan Bindiga, sakamakon yadda Fulani makiyaya da dama suka sauya tsarin nasu zuwa ayyukan kisa da garkuwa da mutane domin neman ku?in fansa a sassa daban daban na kasar.
Jihohi irin su Katsina Zamfara da Kaduna sune akan gaba wajen fuskantar wannan ta’asar, lamarin da yaja hankalin Gwamnati ta tarayya da Jihohi akan hanyoyin da za a bi wajen shawo kan rikicin.
