Tsohon Sakataren Tsaron Amurka Donald Rumsfeld Ya Mutu

Rahotanni daga kasar Amurka na bayyana cewar Tsohon Sakataren Tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ?aya daga cikin manyan wa?anda suka haddasa ya?in Ira?i, ya mutu yana da shekara 88, kamar yadda iyalinsa suka sanar.

Wanda ya yi aiki zamanin shugaba George W Bush, ya kasance babban mai jagorantar ya?i da ta’addanci na gwamnatin Amurka a lokacin.

Dakarun Amurka sun ?addamar da ya?i a Afghanistan bayan harin 9/11. A 2003 Amurka ta mamaye Ira?i.

Mista Rumsfeld ya yi murabus a 2006 sakamakon abin da ya biyo bayan ya?in Ira?i, amma ya kare kansa.

Related posts

Leave a Comment