An Yi Addu’o’in Kwanaki 40 Na Rasuwar Tsohon Shugaban Dakarun Soji

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sojoji sun gudanar da addu’ar 40 ga marigayi Tsohon Shugaban Dakarun Soji Ibrahim Attahiru, tare da sauran manyan jami’ai 10, wa?anda suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin jirgi a Kaduna ranar 21 ga watan Mayun shekara ta 2021.

Addu’ar ta gudana ne bisa jagorancin daraktan al’amuran addinin musulunci na rundunar sojin ?asa, Janar Shehu Mustapha. Mustapha yayi addu’a ga rayukan mamatan su samu rahama, kuma ya ?ara ta’aziyya ga iyalansu.

Yace ya kamata yan Najeriya su ri?a tunawa da cewa kowane rai zai ?an?ani mutuwa, saboda haka akwai bu?atar kowa ya yi rayuwa mai kyau cikin biyayya ga Allah.

Mustapha ya ?ara da cewa an shirya wannan taron ne domin tunawa da marigayi shugaban rundunar soji da kuma sauran jami’an da suka rasu tare da shi.

Sannan Sojojin sun yi addu’ar zaman lafiya da samun nasara Hakanan kuma sojojin sun yi addu’an neman zaman lafiya tsakanin yan Najeriya da kuma nasara ga sojin dake yaki a ?angarori daban-daban na ?asar nan.

Mustapha, yace: “Muna amfani da wannan damar domin yin addu’a ga iyalan mamatan, shugabannin tsaron, da kuma zaman lafiya tsakanin yan Najeriya.” “Muna ro?on Allah ya shiga lamarin mu kan wannan ?alubalen tsaron da ?asar mu ke fuskanta, idan ma wani laifi muka yi wa Ubangiji, muna rokon ya mana gafara.” “Hakanan muna ro?on Allah ya cigaba da kare shugabannin mu, ya taimake su bisa jagorancin su domin su ceto ?asar mu daga halin da take ciki.”

Related posts

Leave a Comment