Tsige Mataimakin Gwamna: Babu Kotun Da Ta Isa Ta Hana – ‘Yan Majalisar Zamfara

Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewa Majilisar Dokoki Jihar ta bayyana cewa babu wata dokar kotu da za ta iya hana ta tsige Mataimakin Gwamna, Mahdi Aliyu Gusau.

Shugaban Kwamitin Ya?a Labarai na Majalisar, Shamsudeen Bosko ne ya fadi hakan a taron manema labarai a Gusau.

A ranar Litinin ne dai wata Babbar Kotun Taraiya ta garga?i majalisar dokokin ta Zamfara kan shirin tsige Mahdi.

Mai Shari’a Iyang Ekwo ne ya yi garga?in bayan da lauyan PDP, Emmanuel Ukala, SAN, da kuma shi Mataimakin Gwamnan su ka shigar da ?ara, inda su ka roki kotun da ta hana majalisar tsige shi.

Amma mai Shari’a Ekwo bai fito ?arara ya bada umarnin hana tsige Mahdi ?in ba.

Sai dai ya ce tunda dai dukka ?angarori biyun sun je kotu, to ba wanda zai ?auki wani mataki yayin da maganar ke kotu.

Sai dai kuma, a taron manema labaran, Bosko ya ce babu wata kotu da za ta iya tsaida su da ga tsige Mahdi ?in, inda ya ?ara da cewa, hanyar da a ka bi taa tsige Mataimakin Gwamnan ta yi dai-dai da sashi na 188(5)(7) na 1999.

A cewar sa, 18 cikin ?an majalisa 24 sun za?i a tsige Mahdi ?in lokacin da aka same shi da badakalar kudaden, rashin biyayya da kuma ?in yin aiyukan da a ka sa shi ya yi.

Related posts

Leave a Comment