Ketare: Mawakin Indiya Lahiri Ya Sheka Lahira

Rahotanni daga kasar Indiya na bayyana cewa Mawa?in Indiya, Bappi Lahiri wanda aka sani da wa?o?in disko da kuma ca?a kwalliya, ya mutu yana da shekara 69 a duniya.

Lahiri wanda ya warke daga cutar korona a watan Afrilun da ya wuce, ya shafe watan da ya gabata a asibiti. Ya rasu ne a jiya Talata.

Salon ki?ansa na disko ya sa masu kallo sun sha?u da wa?o?insa, inda sukan ti?i rawa sosai duk sanda aka kunna wa?arsa.

‘Yan siayasa da ‘yan wasan cricket da ‘yan fim na Bollywood sun yi ta’aziyyar rasuwar, inda da yawa suka dinga tuna wa?o?insa da suka fi so.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya ce ya ka?u da rasuwar Lahiri.

Related posts

Leave a Comment