Kaduna: Nasarar PDP A Zaben Cike Gurbi Nasara Ce Ga Dimukuradiyya – Jam’iyyun Adawa
An bayyana cewar nasarar da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi a zaben cike gurbi na ?an Majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar ?aramar Hukumar Sabon Gari nasara ce ba kawai ga PDP ba sai dai nasara ce ga mulkin dimukura?iyya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban ?ungiyar Jam’iyyun Adawa na ?asa baki ?aya Alhaji Umar Ibrahim Mai Rakumi a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a garin Kaduna.
Mai Ra?umi ya cigaba da cewar wannan nasara da PDP ta samu ya zama tamkar zakaran gwajin dafi a siyasar Jihar Kaduna musanman a za?ukan kananan hukumomin dake tafe a Jihar.
Umar mai Ra?umi wanda a hannu guda shine Sakataren jam’iyyar Labour na kasa ya kara da cewar jama’a a yanzu suna ?ara samun wayewa ta fuskar siyasa, ta hanyar da su da kansu suke zaben abin da ya dace da su, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, suke duba cancanta kuma wannan shine hanya mafita na samun nasara.
Dangane da batun ko ba?in jinin El Rufa’i ne ya haifar da faduwar APC a Sabon Gari, Umar mai Ra?umi ya ce jama’ar Jihar Kaduna suke da wuka da nama da rariyar tace dukkanin abin da bai musu daidai ba, inda zasu yi amfani da damar da suke da ita wajen maganin duk wanda ya cuta musu.
Daga karshe Mai Rakumi ya yi kira ga dukkanin jama’ar Najeriya da su tabbatar sun sabunta katin zabensu a aikin sabunta katin da hukumar INEC za ta yi, domin samun makamin ‘yanci a hannun su.
