Tsaro: Za A Dauki Kuratan ‘Yan Sanda 10,000 Aiki

Labarin dake shigo mana daga Abuja na bayyana cewar Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingya?i, ya bayyana cewa nan da wata ?aya za a ?ara ?aukar kuratan ‘yan sanda 10,000.

A zantawarshi da manema labarai a Abuja ya ce za a ?ara ?aukar su ne domin cika alwashin da aka yi na cewa za a ?auki ‘yan sanda 40,000 aiki, kafin ?arshen zangon Buhari na biyu.

Dangane da ?arin girman da aka yi wa tsohon Ibrahim Magu, Maigari ya ce gwamnati na duba yiwuwar aiki da shawarwarin rahoton, kuma don an ?ara masa girma ya yi ritaya, hakan ba zai hana idan an same shi da laifi a hukunta shi ba.

Related posts

Leave a Comment