Rahoton dake shigo mana daga Jos babban birnin jihar Filato na bayyana cewar Gwamnan jihar Simon Lalong, ya ce yana goyon bayan Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma dan takarar shugaban kasa na 2023, ya kuma ce ba zai bi bayan wani dan takara daga arewacin Najeriya ba.
Lalong ya yi wannan ikirarin ne a Jos, lokacin da Amaechi ya je jihar don jan hankalin wakilan jam’iyyarsu yayin da zaben fidda gwani ya ke kunno kai.
A cewar Lalong, Amaechi ya taka babbar rawa a jiharsa don haka zai samu goyon baya daga duk shugabannin Filato, ciki har da tsohon kakakin majalisar tarayya da ‘yan majalisar jihar.
Ya ce Amaechi ne kadai zai iya kawo karshen rashin tsaro A wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a ranar Asabar, an yanko inda Lalong ya ke cewa: “Amaechi ya na da duk halayen shugaba na kwarai kuma shi ne zai ceto kasar nan daga matsalar rashin tsaro sannan ya ciyar da sauran bangarorin kasar nan gaba.
