Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa rundunar ?an sanda ta ce tana aiki tu?uru don tabbatar da kare rayukan jama’ar babban birnin tarayya Abuja, inda hare-haren ?an bindiga ke ?ara zafafa a baya-bayan nan.
Rundunar ta ce tuni babban Sifetan yan sandan ?asar ya ba da umarnin ?ara baza jami’an tsaro a sassan birnin don tabbatar da wannan aniya.
Rundunar ta kuma bu?aci jama’a a birnin su taimaka mata da bayanan sirri domin samun nasarar abun da aka sanya a gaba.
A baya bayan nan dai ana ta samun karuwar hare-haren yan bindiga a Najeriya, musamman a garuruwan da ke kewaye da birnin, inda maharan ke kashe jama’a, suna garkuwa da wasu da dama.
