Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake caccakar abokin hamayyarsa Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
Atiku ya caccaki Tinubu kan ikirarin cewa ya ba wa jigon na jam’iyyar APC damar tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa a 2007, inda ya ce da gaske Tinubu ne ya nemi hakan, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.
A wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli a gidan talabijin na Arise, ya yi ikirarin cewa Tinubu ya nemi ya yi takarar mataimakinsa a karkashin jam’iyyar Action Congress, tare dashi amma ya ki amincewa saboda ganin hakan ya saba tsarin siyasar addini.
A martaninsa, Tinubu ya zargi Atiku da tafka karya, inda ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ne ya nemi ya ba shi mukamin.
Atiku ya ce kwakwalwar Tinubu ta samu matsala a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya fitar, ya bayyana cewa, ba wai karya kawai Tinubu ya tafka ba, akwai alamu ya gaza tunawa.
“Ba za mu ce Bola Tinubu ya yi karya ba. Maimakon haka, muradinmu ne mu ba shi uzuri kuma mu dauka cewa kwakwalwarsa ba ta nan kamar yadda take a da.”
