Tsaro: Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu – Shugaban Dakarun Soji

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban dakarun soji Janaral Farouk Yahaya ya gudanar da wani taro da manyan kwamandojin sojin kasar.

Da yake bude taron, Janaral Yahaya ya ce za su yi dukkanin mai yiwuwa wajen kare ‘yanci Najeriya ta yadda ba za ta ruguje ba.

Taron ya tattaro baki manyan kwamandojin rundunonin sojin kasar da zimmar bitar inda aka fito da inda aka nufa, dangane da ci gaban da aka samu a fannin tsaro.

Janaral Yahaya ya ce babu shakka akan rawar gani da aka taka wanda har yabo dakarun kasar suka samu daga cibiyar dake sa ido kan ta’addanci a duniya dangane da yadda aka cimma gagarumar nasara wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Related posts

Leave a Comment