Sanata mai wakiltar maza?ar Imo ta yamma a majalisar Dattawa Sanata Owelle Anayo Rochas Okorocha, ya bayyana cewar bai da wani buri a yanzu da ya wuce ganin kowane yaro ya samu gajiyar ilimin zamani.
Okorocha ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyoyin Tsofaffin daliban na gidauniyar Okorocha ?arkashin jagorancin Injiniya Adamu Suleman da na sabuwar Najeriya bisa jagorancin Alhaji Audi Mohammed a ziyarar da suka kai masa a Unity house dake birnin tarayya Abuja.
Sanata Okorocha ya ?ara da cewar muddin dukkanin jama’a suka bada goyon baya wajen limantar da dukkanin yara ba tare da la’akari da banbancin addini ko kabila ba babu shakka kasar Najeriya za ta kai ga wani matsayi abin girmamawa.
Rochas Okorocha wanda a kwanan nan Masarautar Daura ?ar?ashin jagorancin Sarki Faruoq Umar ta nada shi Sarautar Maga Alherin Daura, hakazalika an na?a matarshi Uwargida Nneoma Nkechi Okorocha Sarautar Zinariyar Kasar Hausa, ya bayyana cewar cibiyar tashi ta Rochas Foundation ta ?auki nauyin ilmantar da yara da yawansu ya kai kimanin Miliyan 13 da rabi a fadin kasar da makwabtan kasashe.
Sanata Okorocha ya nuna godiyarshi ga mai Martaba Sarkin Daura Farouk Umar Farouk bisa ga wannan sarauta da ya bashi ta Maga Alherin Daura.
Ya kuma yi amfani da wannan dama inda ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar lokacin bukukuwan sallah, inda ya shawarci jama’ar Musulmi da suyi amfani da wannan lokaci wajen gudanar da addu’o’i ga shugabanni da ?asa domin samun zaman lafiya.
Tun farko da suke bayani injiniya Adamu Suleman da Alhaji Audi Mohammed, sun bayyana makasudin ziyarar tasu ga Sanatan shine domin taya shi murna akan Sarautar da ya samu a masarautar Daura dake jihar Katsina.
