Labarin dake shigo mana daga Abuja na bayyana cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce Kiristoci za su yaki tikitin musulmi da musulmi na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023 da addu’a.
Babachir Lawal ya bayyana hakan ne yayin wani taro na shugabannin Kiristocin Arewa da aka yi a ranar Juma’a, a babban birnin tarayya Abuja.
Da ya ke tsokaci kan batun, Lawal ya ce: “Tabbas, akwai makarkashiya ta siyasa, addini da na tattalin arziki da kuma danne kiristocin arewacin Najeriya. Amma a shirye muke. “Za mu kare kan mu.
Katin zabe na PVC da addu’a ne makaman da muka zaba kuma za mu yi amfani da su sosai a 2023.” Lawal ya ce ajandar tikitin musulmi da musulmi yanzu ma ta fara wanzuwa, ya kara da cewa kiristoci ba za su lamunci hakan ba.
Ya cigaba da cewa yin tikitin musulmi da musulmi lamari ne da aka dade ana shiryawa don haka batun cancanta yasa aka zabi mataimakin ba gaskiya bane.
