Tsaro: Buhari Ya Kalubalanci ‘Yan Najeriya Su Ba Dakarun Soji Hadin Kai

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa ya yi kira ga ‘yan Najeriya cewa su yi amanna da sojojin ?asar cewa za su iya kawo ?arshen matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a ?asar nan.

Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke bu?e Gasar Wasannin Motsa Jikin Sojojin Ruwa Na 12, wato LAGOS 2023.

Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da jajircewa wajen ganin sun samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma sun kawar da ?alubalen da ya dabaibaye ?asar nan.

Ya ce dukkan ?angarori na tsaro za su ci gaba da ?aukar dukkan matakan da su ka dace wajen tabbatar da kare lafiyar dukkan al’ummar ?asar nan.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana bu?ata da muhimmancin ha?in kai da aiki tare tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro da kuma al’ummar ?asar nan baki ?aya.

Shugaba Buhari wanda ya sabunta sabuwar cibiyar wasannin Sojojin Ruwa, wadda aka gina kwanan nan, ya jinjina wa Shugaban Sojojin Ruwa CNS Awwal Gambo, bisa gina cibiyar bun?asa wasannin da ya yi.

“Tsawon shekaru kenan wasanni sun kasance hanyoyin ?arfafa dangantaka da jituwa tsakanin sojoji tare da cusa ?a’a a cikin sojoji. Ina mai tabbacin cewa wa?annan wasanni da za a yi za su ba sojojin ruwa damar cimma dukkan ?udurorin da ke gaban su.”

Buhari ya kuma yi kira da a yi amfanin da cibiyar wasannin ta hanyar da ta dace.

Related posts

Leave a Comment