An shawarci shugaban kasa Muhmmadu Buhari na da ya sauya sunan jami’ar Nsukka (UNN) zuwa sunan marigayiya sarauniyar Ingila domin cigaba da tuna wa da ita a tarayyar Najeriya.
Wannan kira dai na fitowa ne daga bakin tsohon dan takarar shugaban kasa a APC, Adamu Garba II a ranar Juma’a 9 ga watan Satumban 2022.
A wani rubutu da ya yi a Twitter, Adamu Garba ya ce kamata ya yi a ce gwamnatin Najeriya ta sauya sunan jami’ar UNN zuwa ta Sarauniya Elizabeth II wadda ta rasu kwanakin baya.
A cewarsa, wannan ne hanya mafi sauki da za a ke tunawa da sarauniyar da irin ayyukanta kasancewarta sarauniya a ?asar da ta mallaki Najeriya a shekarun baya.
Adamu ya kuma ce idan da shine shugaban kasa, zai ba da hutun kwanaki uku domin jimamin mutuwar sarauniyar da ta fi kowane sarki jimawa a karagar mulki. A rubutun nasa guda biyu a Twitter, ya ce:
“Domin ci gaba da tunawa da sarauniya Elizabeth, ya kamata mu sauya sunan jami’ar Najeriya ta Nsukka zuwa jami’ar sarauniya Elizabeth ta Najeriya tun da itace jami’ar farko a Najeriya. “Idan nine shugaban Najeriya a yau, zan ayyana kwanaki uku na jimamin mutuwar sarauniya Elizabeth II ta kasar Ingila.
