Kungiyar Yan’jarida reshen Jihar Bauchi ta raba kayan tallafi na dubban naira ga marasa lafiya da suke kwance a Asibitin kwararro na Jihar da Asibitin Bayara na cikin garin Bauchi, A ci gaba da bikin mako na Yan’jarida na shekarar 2020 da yake gudana a halin yanzu.
A lokacin da yake mika kayan tallafin a Asibitocin Shugaban Kungiyar reshen Jihar Kwamared Umar Sa’idu yace rana kayan anyi shine domin a tallafa ma marasa galihu da Kuma tausayawa masu fama da rashin lafiya da wasu kayayyakin domin suma suji dadi a ransu.
Kana yace Kungiyar tayi haka ne, wanda daya ne daga cikin irin abubuwanda Kungiyar zata yi a lokaci bikin makon ta na shekara-shekara.
Sa’idu yayi fatan Allah ya basu lafiya da kuzari, yace Kungiyar baza tayi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da ayyuka na jin kai ba, ga al’umma. Marasa lafiyan da suka samu wan nan tallafi sun yaba ma shuwagabannin Kungiyar da yi masu addu’an fatan alkhari, Allah ya taimaki aikin Yan’jarida ya Kuma tsare masu mutuncinsu baki daya.
Kungiyar Har’ila yau takai ziyarar ban girma fadar Mai martaba Sarkin Dass. Alhaji Usman Bilyaminu Othman, Wanda shine Uban Kungiyar reshen Jihar Bauchi, kaamarade Umar Sa’idu da yake ma Mai martaba jawabin makasudin wan nan ziyara, yace Kungiyar tana da al’ada na girmama manya musamman ma iyayen kasa wanda sune ake neman adduarsu domin samun ci gaban al’umma, tare da samar da wanzuwan zaman lafiya mai dorewa.
Sarkin na Dass ya yaba ma shuwagabanin Kungiyar da irin jajircewansu wajen tafiyar da shugabanci mai adalci kana yayi ma Kungiyar addu’ar ci gaba da ayyukansu na alheri a ko da yaushe, musamman ta wajen watsa labarai na gaskiya da fadakar da al’umma da Kuma wayar masu da kai.
Haka nan Kungiyar ta gudanar da taron manema labarai a sakatariyar karamar hukumar Bogoro domin karrama Tsohon dan’ta wanda shine Shugaban karamar hukumar a halin yanzu Mr. Iliya Habila, inda Shugaban Kungiyar ya zayyana irin ayyukan da kungiyar zata gudanar a cikin kwanaki bakwai da zatayi tana biki makon nata a fadin Jihar Bauchi.
Daga bisani Shugaban karamar hukumar Iliya Habila yace Yan jarida suna ilmantar da mutane ta wajen bada rahotanni su na gaskiya, kana yaja hankalin su da su rika shiga lungu da sako musamman kauyuka inda ake samun labarai dake da alaka da al’umma kai tsaye, acewarsa Yan’jarida sune idon al’umma.
