Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana hukumar kiyaye hatsurra FRSC ta soma bincike domin gano abin da ya yi sanadiyyar da tawagar Goodluck Jonathan tayi hadari a kan titin Abuja.
Bayanai sun nuna cewa ana tunanin motocin tsohon shugaban kasar sun yi gudun ganganci ne lamarin da ya kai ga afkuwar hatsarin.
Babban jami’in hukumar mai kula da shiryyar birnin tarayya Abuja, Samuel Ogar Ochi ya bayyana hakan lokacin da aka yi hira da aka zanta dashi.
Ogar Ochi ya tabbatarwa manema labarai cewa za a gudanar da cikakken bincike na musamman domin gano abin da ya kai ga hadarin.
