Gamayyar Kungiyar Matasan tarayyar Najeriya ta bayyana cewar ko shakka babu tsohon Dogarin marigayi Tsohon Shugaban ?asa Marigayi Sani Abacha Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya shine mafita wanda zai iya ceto kasar daga halin da take ciki idan aka za?e shi Shugabŕn ?asa.
Kungiyar Matasan ta yi wannan kiran ne a yayin wani taron manema labarai da ta kira a garin Kaduna.
Da yake jawabi a yayin taron shugaban gamayyar Kungiyar Matasan Najeriya na kasa Alhaji Abdullahi Abubakar Wali ya bayyana cewar Najeriya ta kama hanyar rugujewa kuma tabbas ana bukatar jarumi da zai ceto ?asar, kuma babu wanda ya dace da hakan sai Hamza Al-Mustapha.
“A fili yake dukkanin wa?anda Manyan Jam’iyyu suka tsayar takarar shugabancin kasa tsofaffi ne wa?anda sun tashi aiki kuma ba za su iya ba, bisa ga haka muna kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da batun Jam’iyya su za?i cancanta, kuma Hamza Al-Mustapha shi ya dace domin dawo da ?asa kan saiti”.
