‘Yan Najeriya Sun Matsa In Fito Takarar Shugabancin Kasa – Gwamnan Akwa-Ibom

Rahoton dake shigo mana daga Uyo babban birnin jihar Akwa-Ibom na bayyana cewar Gwamna Udom Emmanuel na jihar ya ce ya amsa kiran wasu yan Najeriya ta bakin kungiyar kare ha??in bil adama ‘Brekete Family’ na fitowa takarar shugaban ?asa a 2023.

Emmanuel ya tabbatar da amincewa da kiran yan Najeriya ne a fadar gwamnati dake Uyo, ranar Alhamis da yamma, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Gwamnan ya amince da haka ne lokacin da kafar Talabijin da Radiyo Brekete Family Radio/TV ta mi?a masa Fam ?in takara na jam’iyyar PDP da ta siya masa kan Miliyan N40.

Gwamnan ya mi?a godiya ga wanda ya kafa kafar labaran, Ahmed Isah, da sauran yan tawagarsa, wa?an da suka yi karo-karo suka siya masa Fam ?in takarar Kujerar Shugabancin kasar.

“Na yaba da wannan karamci, ina mai tabbatar muku da cewa na amince da wannan Fam, na amince da Fam ?in takarar shugaban ?asa. Ba abin da yan Najeriya zasu ha?a kai su nema na yi watsi da shi.”

“Gaskiya lokacin da na ji labarin kun fara shirin siya mun Fam, na tambayi kaina, ta ya zaku iya ha?a Miliyan N40m? Amma yau ga shi mafarkin ku ya zama gaskiya.”

“Muna da mutane sama da miliyan 200m a Najeriya, amma kuka za?e ni don girmamawa, na ji ?a?i sosai, ina ?ara yaba wa wannan tawaga, sannan ina yaba wa yan Najeriya bisa kwarin guiwarsu a kaina.”

Related posts

Leave a Comment