Tirkashi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Kashe Buhari Da El Rufa’i

A sabon bidiyo da suka fitar ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna sun yi barazanar sacewa da kashe Shugaba Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Barazanar dai na zuwa ne makwanni bayan da wasu ’yan ta’adda suka kai hari kan tawagar motocin shugaban ?asa yayin da suke kan hanyar zuwa garin Daura a Jihar Katsina, gabanin tafiyarsa hutun Sallar layya.

A cikin bidiyon, ’yan ta’addan sun kuma yi bugun kirjin cewa za su ruguza kasar nan, sannan za su kashe wasu daga cikin fasinjojin da ke hannunsu su kuma sayar da sauran.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa, idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Najeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu.

Related posts

Leave a Comment