NEJA: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Ci Rayuka

Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewa mutum ?aya ya rasu sannan wani ya jikkata bayan kifewar kwale-kwale a Kogin Zumba na Jihar ?auke da ‘yan kasuwa kusan 50.

Mutanen sun fito daga kauyen Shiroro zuwa kasuwar Kwata a ?aramar Hukumar ta Shiroro.

Rahoton ya ce mutum shida ne kawai aka samu damar cetowa daga fasinjojin da ke cikin jirgin ruwan.

Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Ibrahim Inga, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce bai samu bayanin adadin wadanda abin ya ritsa da su ba.

Sarkin Ruwa na Kwatar-Zumba, Umar Isah, ya fada wa manema labarai cewa injin jirgin ruwan da ke dauke da fasinjojin ne da suka hada da mata da kananan yara da dabbobi da sauran kayan amfanin gona ya samu masala a tsakiyar kogin, inda hakan ya janyo kifewar sa.

Related posts

Leave a Comment