Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Ogun na bayyana cewa Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya kalubalanci matasan Najeriya da su tashi su karbi ragamar shugabancin kasar nan daga hannun tsofaffi.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli yayin wata tattaunawa ta musamman da tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Segun Odegbami, a gidan rediyon Eagle7 Sports 103.7 FM da ke Abeokuta ta jihar Ogun.
Kalaman tsohon shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce na rasa matashi mai tasiri a takarar shugaban kasa gabanin babban zaben 2023.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa ya kamata matasan Najeriya su yi watsi da taken “manyan gobe,” yana mai cewa “goben” ba za ta taba zuwa ba.
Ya ce wasu gurbatattun shugabanni za su ruguza abin da ake kira goben matasa idan matasan suka kasa tashi tsaye wajen kwace makomarsu a hannunsu.
“Shawarata ga matasan Najeriya ita ce, kada ku bari wani ya ce muku ku ne manyan gobe. Idan kuna jiran sai gobe kafin ku karbi ragamar shugabanci, to goben ba za ta zo ba. Za su halaka ta.
