A matsayinsa na shugaban kasar Najeriya, an sha caccakar Buhari saboda kasancewarsa shugaban kasa mafi yawan tafiye-tafiye da aka taba samu a Afrika ta yamma.
A cewar jaridar The Punch, Buhari ya ziyarci kasashen duniya 40 a matsayin shugaban kasa kuma ya yi tafiye-tafiyen kasashen waje 90 a shekaru 8 a Najeriya.
Da ake nazarin shekaru 8 da ya yi a matsayin shugaban kasa, Buhari ya ziyarci akalla kasashe 43 a fadin duniya.
Kasashen da Buhari ya ziyarta sun kasance a fadin kasashen duniya kuma yawanci ziyar aiki, na ganin likita da kuma sauke farali ne.
