Gyaran Fuska A Dokar Zabe: Bukatar Buhari Ta Raba Kawunan ‘Yan Majalisa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an samu rarrabuwar kawuna a ranar Talata kan kiran da majalisar dattawa ta yi na yin muhawara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na haramta sashe na 84(12) na dokar zabe.

Rikicin dai ya faro ne a lokacin da Sanata George Sekibo daga jihar Ribas, yayin da yake dogaro da doka ta 10 da 11 na majalisar dattawa, inda ya tunawa takwarorinsa yadda ayyuka daban-daban na bangarorin gwamnati guda uku suke.

Ya kara da cewa hukuncin da kotun ta yanke, wanda ya soke matakin da Majalisar ta dauka, wani mummunan lamari ne da bai kamata a bari ya tafi haka ba. Ya ce idan har aka bar batun, jam’iyyun siyasa za su iya kalubalantar matsayin majalisar a gaban Kotuna.

Sekibo ya bukaci takwarorinsa da su dakatar da sauran ayyukan majalisar na ranan domin zama tare da tafka muhawara kan batun.

“Wannan batu yana da matukar muhimmanci. Wadanda suka je kotu don kalubalantar matakinmu ba su hada da mu a matsayin wadanda ke da sha’awar kan batun ba.

Ba mu ma san cewa wani lamari na gaban kotu ba. “Ba zato ba tsammani, sai aka ce mana an yanke hukunci, nan take Gwamnatin Tarayya ta dauke shi.

“Hakan na da hadari kuma muna bukatar daukar mataki cikin gaggawa. Wannan na da mahimmanci don daidaita irin wadannan abubuwan.”

Related posts

Leave a Comment