Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na ?asar Amurka na bayyana cewar Asusun bada lamuni na Duniya ya ce da yiwuwar tattalin arzikin Saudiyya zai iya zama mafi habbaka a duniya a wannan shekarar yayin da tattalin azrikin duniyar ke fuskantar koma baya.
A cewar Bankin masarautar na duba yadda za ta cimma kashi 7.6, wanda bukatar mai da ake da ita a duniya za ta matukar taimakawa da kuma habbakar bangarorin da ba na mai ba.
Karin bukatar da ake da ita ta makamashi – saboda rikicin Ukraine – ya taimaka wa manyan kasashen duniya da ke da mai wajen farfadowa daga illar da Covid-19 ta yi musu.
Har yanzu hauhawar kayan farashi a kasar bai fi kashi uku ba kacal cikin 100.
