?an Najeriya sun auka cikin duhu a sassan ?asar sakamakon tafiya yajin aikin da ma’aikatan wutar lantarki na ?asar suka fara.
Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, ranar Laraba da safe.
Sun fara kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke fa?in ?asar.
Wani jami’in kamfanin ya shaida wa BBC cewa suna fatan gwamnati za ta shiga cikin lamarin, idan ba haka ba kuwa to kowa zai zauna a cikin duhu.
Yajin aikin ya samo asali ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin ?ungiyar ?wadago ta Ma’aikatan Lantarkin da kuma Kamfanin Dillancin Lantarki.
Ma’aikatan kamfanin dillancin lantarkin dai na son a dakatar da tsarin aikin da ake bi na ci gaban ma’aikata.
Da umarnin da hukumar gudanarwar kamfanin dillancin lantarkin ta bayar ta yin jarrabawar ?arin girma ga wa?anda suka kai mu?amin mukaddashin babban manaja da za su yi gaba zuwa mu?amin mataimakin Janar Manaja.
A daina nuna bambanci ko wariya ga ma’aikatan da suka fito daga ofishin shugaban ma’aikata na tarayya, wadanda ba a barinsu su yi aiki a wasu sassan bangaren samar da wutar lantarki.
Sun ce ba za su janye yajin aikin ba har sai gwamnati ta amsa bukatunsu.
