Cin Zarafin Dan Kallo: ‘Yan Sanda Sun Garga?i Ronaldo

‘Yan sanda sun ja kunnen Cristiano Ronaldo, bisa wani faifan bidiyon da ya nuna dan kwallon ya wafce wayar dan kallo ya buga da kasa.

‘Yan Sandan Merseyside sun ce sun yi wa dan wasan mai shekara 37 tambayoyi, sun kuma gargadeshi kan laifin da ya shafi cin zarafi da lalata dukiya.

Jami’an tsaron sun tabbatar da faruwar lamarin sun kuma damu da halayar a karawar da United ta yi da Everton ranar 9 ga watan Afirilu.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila itama ta ce za ta gudanar da nata binciken nan gaba.

Related posts

Leave a Comment