Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewa an yi wata gobara a gidan sanannen malamin nan Sheikh Dakta Ahmed Abubakar Gumi da ke garin Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewar lamarin afkuwar gobarar ya faru ne a ranar Asabar da rana.
Babu tabbaci kan abin da ya jawo gobarar hakazalika babu ?arin bayani kan ko akwai wanda ya samu rauni ko kuma ya rasa ransa.
Wani bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna yadda ake ?o?arin kashe gobarar.
Haka kuma a cikin bidiyon an ga malamin na duba sassan gidan da gobarar ta shafa
