Masu Yi Wa Kasa Hidima Ne Za Su Yi Amfani Da Na’urar Tantance Masu Zabe – INEC

Hukumar Za?e Mai Zaman Kanta ta ?asa ta ce Masu yi wa ?asa hidima ne kadai za su yi amfani da na’aurar tantance masu ka?a ?uri’a ta BVAS a ranar za?e.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyoyin da ake bayar da horo ga ma’aikatan wucin-gadi da hukumar ta ?auka dan gudanar da aikin za?en, a Abuja babban birnin ?asar.

Farfesa Yakubu ya ce domin samun nasarar gudanar da za?en hukumar na bu?atar ha?in kan masu yi wa ?asa hidima.

Haka kuma shugaban hukumar ya yi kira ga masu yi wa ?asa hidimar da su zama masu biyayya ga Najeriya da ‘yan Najeriya ba jam’iyya ko wani ?an takara ba.

Ya sake jajjada musu cewa kada su yadda su bayar da na’uara BVAS ?in ga wani jami’in za?en, yana mai cewa za a ri?a bibiyar kowane ?aya daga cikinsu.

Yakubu ya ce “Najeriya ta yi sa’a da ta samu ‘yan ?asa irinku. Babu yadda za a yi INEC ta gudanar da za?e ba tare da masu yi wa ?asa hidima ba. Kun zama dole sai da ku ake gudanar da za?en Najeriya. ba za mu iya gudanar da za?e ba tare da taimakonku ba.”

“Dan haka mun dogara a gareku da sauran ma’aikata.Kuma ku ne za ku yi amfani da abu mafi muhimmanci (BVAS) a harkar gudanar da za?en a kowacce rumfar za?e, inda kowanne mutum zai je domin ka?a ?uri’arsa. saboda haka kowanne daga cikinku zai rantse cewa zai zama ?an ba-ruwanmu a za?en. Za ku yi biyayya ne ga Najeriya ba wata jam’iyya ko ?an takara ba. Ku ne wakilan INEC a rumfunan za?en. Dan haka ku ne sarakai a rumfunan za?e.

Related posts

Leave a Comment