Kano: Kotu Ta Dage Shari’ar AbdulJabbar Zuwa Watan Satumba

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Kotun dake saurarar karar da gwamnatin Kano ta shigar akan Shehun Malami AbdulJabbar ta ?age sauraron ?arar har zuwa ranar 2 ga Satumban 2021.

A ranar Laraba ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ?age sauraron ?arar bayan da aka yi zama na biyu tun fara shari’ar a birnin Kano.

Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ?arar Malam Abduljabbar kan zarginsa da yin kalaman ?atanci ga Annabi SAW.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a fa?in ?asar ba ma jihar Kano ka?ai ba

Mai Shari’a Sarki Yola ya ce ya ?age sauraron ?arar ne saboda duk hujjojin da aka gabatar sun yi masa tsauri ya yanke hukunci nan take.

Ya ?ara da cewa akwai bukatar ya sake duba su, sannan ya san matsayar da zai ?auka kan sabbin tuhume-tuhumen da gwamnati ta gabatar a zaman kotun na yau kan Sheikh Abduljabbar, ku kuma mafani da tuhume-tuhumen farko da aka gabatar.

Lauyoyin gwamnati sun bu?aci a ba su dama su karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka je da su a kan Sheikh Abduljabbar, amma nasa lauyoyin suka soki hakan.

Lauyoyin Abduljabbar sun ?alubalanci takardar sabbin tuhume-tuhumen da lauyoiyin gwamnati suka gabatar.

Barista Saleh Bakaro wanda shi ne lauyan da yake jagorantar ?angaren Abduljabbar, ya ce gaba daya lauyoyin SAN din da gwamnati ta dauko ba su da hurumi a tsarin dokar aikin lauya na shiga zuwa ?aramar kotu.

“Daga babbar Kotun Tarayya ne aka yarda SAN su fara zuwa kotu. Sannan sabbin tuhume-tuhumen da suka bayar ya sa?a da tsarin dokar shari’ar Musulunci.

“Ba a yarda mutum ya sake shigar da tuhuma ko ?ara kan wata da ake saurara ba, bayan gabatar da shaidar farko a tsarin dokar Shari’ar Musulunci,” a cewar Bakaro.

Su kuwa lauyoyin ?angaren gwamnati sun ce kamata ya yi lauyoyin Abduljabbar sun dakata a gama karanto sabbin tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda ake ?arar kafin su kawo wata suka kan lamarin.

Sun ce a bisa doka wajibi ne a karanto cajin wanda idan an kammala ne sannan ewani bangare zai iya suka ko goyon bayan a ci gaba da shari’a.

Barista Surajo Sa’ida SAN mai jagorantar lauyoyin gwamnati ya dogara ne da Sashe na 390 ?aramin sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda a don haka ya bu?aci lauyan Abduljabbar ya janye sukar da ya yi har sai banayn an kammala karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka gabatar wa kotu.

Lauyoyin Abduljabbar sun ce sashen da lauyoyin gwamnati suka dogara da shi, na magana ne kan cajin da aka gabatar tun ranar farko da aka gabatar da Abduljabbar a kotun ranar 16 ga watan Yunin da ya gabata.

A ranar fara sauraron ?arar an karanta masa tuhumar da ake masa ne ta farko ta ‘yan sanda, wanda kuma bai amsa aikata laifin ba, don haka ya riga ya amsa ?ara, wanda hakan ke nuni da an fara shari’a.

Don haka a cewarsu sashe na 390 da lauyoyin gwamnati suka gabatar ba shi da hurumi a wannan shari’a da ake yi, in ji Bakaro.

To bayan ?aukar lokaci yana rubuce-rubuce ne sai Alkai Sarki Yola ya ce yana bukatar karin lokaci don sakae nazartar tuhume-tuhumen da kuma hujjojin da bangarorin biyu suka gabatar masa.

Ya ce zai yi hana ne “don kare mutuncina da darajar aikina, da kuma adalcin da aikina ya bu?ace ni da yi,” in ji shi.

Daga hakan ne kuma ya bayar da zabin ranaku uku na 1 ko 2 ko 6 ga watan Satumban 2021 a matsayin ranar komawa kotu, inda aka ?arshe aka za?i 2 ga watan Satumban.

Related posts

Leave a Comment