Tabbas Mukin Buhari Alheri Ne Ga Najeriya – Shehun Borno

Mai Martaba shehun Shehun Borno ya bayyana shugaba buhari a matsayin babbar kyauta daga Allah.

Mai martaba shehun borno ya bayyana haka ne a lokacin da Shugaban Majalisar dattawa ya kai masa ziyara cikin fadar shi dake jihar Borno.

Sarkin ya bayyana farin cikinsa na mika wuyan yan ta’addan Boko Haram

Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi, a jiya Litnin, ya ce mutanan jihar Borno sun yi sa’an samun Shugaba Muhammadu Buhari matsayin shugaban kasa saboda gwamnatinsa ta rage ta’addancin boko haram sosai.

Shehun ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan, da ya kawo masa gaisuwan ta’aziyyar rashin ‘yayansa.

Ya ce al’ummarsa ta sha bakar wahala sakamakon rikicin Boko Haram amma sun yi sa’a gwamnatin shugaba Buhari na hanyan kawo karshen rikicin.

A cewarsa, dakarun Sojin Najeriya sun kwace dukkan kananan hukumomin dake karkashin Boko Haram a baya kuma mutane sun koma rayuwarsu kamar yadda suka saba a jihar.

Muna rokon ubangiji Allah ya kara bamu zaman lafiya a cikin kasar mu Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment